1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaman doya da manja tsakanin Nijar da Faransa

Mahaman Kanta Abdoulaye Mamane
August 29, 2023

A yayin da dangantaka ke ci gaba da tsami tsakanin gwamnatin mulkin sojin Nijar da kuma Faransa, masana diflomasiyya na gargadin kasashen biyu su guji jefa al'umma cikin rudani.

https://p.dw.com/p/4Vizc
Niger Niamey | Zanga-zangar kin jinin Faransa I Niamey I ECOWAS
Masu zanga-zangar kin jinin Faransa da ECOWAS a Jamhuriyar NijarHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a karshen makon jiya a daidai lokacin da ake cikar kwanaki 30 da juyin mulki a Nijar, masu zanga-zangar da ke goyon bayan soji sun sha nanata matsayarsu ta amincewa da wadanda suka karbe mulki da tsinin bindiga a ranar 26 ga watan Yuli na 2023.

Duk da yake bai bayyana a gaban dubban masu goyoyn bayansa ba, Janar Abdourahmane Tchiani madugun juyin mulkin ya aike da tawagar memebobin majalisarsa ta CNSP don yi wa masu zanga-zangar godiya, sai dai sakon da ya fi fitowa fili shi ne na tafiyar Faransa daga kasar, inda daya daga cikin membobin majalisar koli ta mulkin sojin ya bayyan karara da cewa "Kokuwarmu ba za ta kare ba har sai mun ga ranar da aka ce ba sojojin Faransa ko daya a cikin Nijar, mun gaya masu da su ba mu kasarmu."

Faransa ta yi kememe a Nijar bayan cikar wa'adin da aka dibar mata

Gwamnatin Faransa ta ki amincewa da sojojin da suka yi juyin mulki, ta kuma ki ta janye jakadanta daga birnin Niamey bayan cikar wa'adin da masu karfin ikon Nijar suka dibar masa na tattare nasa-ya-nasa ya bar kasar, hasalima Faransar cewa ta yi tana goyon bayan hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Karin Bayani:Matsin lamba kan sojojin da suka yi juyin mulki

Wannan matakin ya ba wa masana harkokin diflomasiyya da dama irinsu Ambasador Sulaiman Dahiru masanin harkokin diflomasiyya a Afirka mamaki, wanda ya ce "Ban taba ganin an ce jakada ya fita daga kasa kuma kasar da ta turo shi ta ki ta janye shi ba, saboda hujjar cewa gwamnatin da ta bukaci ya fita ba halasracciyar gwamnati ba ce."

Faransa da Nijar an shiga tsamin dangantakar diflomasiyya

Masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Niamey
Masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a NiameyHoto: AFP/Getty Images

A Nijar 'yan siyasa da kungiyoyin fafutikar kare hakin dan Adam na caccakar matakin, wasu na ganin haka a matsayin yunkuri na taka 'yancin da keta haddin da kasar take da tun bayan samun 'yancin kai a 1960, duk da yake wasu na cewa tun fil-azal Nijar bata karbi 'yancin kai ba daga Faransar. Su kuwa masu adawa da hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum kamar Habibou Kane Kadaoure, shugaban jam'iyyar SDR Sabuwa na ganin sakaci ne daga gwamnatin da ta shude da ta bai wa Faransa damar baje kolinta a Nijar yadda take so, wanda suka sa amintaka tsakanin Faransa da Nijar ta yi karfi, saboda haka ba zai yiwu ta gaggauta ficewa daga Nijar ba.

Karin Bayani: Sabuwar baraka tsakanin Nijar da Faransa

Takon saka mafi tsanani tsakanin Nijar da Faransa a tarihin juye-juyen mulki

Kamfanin hakar Uranium din Faransa a Nijar Areva da ya koma Orano
Kamfanin hakar Uranium din Faransa a Nijar Areva da ya koma OranoHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Faransa ta yi sassauci ga daukacin juye-juyen mulkin da aka sha gudanarwa a Nijar shekaru da dama, ta ci gaba da huldarta ta fannin diflomasiyya da tattalin arziki da kasar duk kasancewarta karkashin mulkin Janar Salou Djibo da ya kifar da mulkin Tandja Mamadou,  ya sa kafarsa a fadar Elysee, ya yi ganawar keke-da-keke da tsohon shugaba Nicolas Sarkozy a taron Faransa da wasu shugabannin Afirka a cikin watan Yulin 2010, lamarin da ya sha ban-ban da halin da Nijar ta shiga a yanzu.

Wannan dai baya rasa nasaba da manufofin Janar Tchianina kokarin sake duba yarjejeniyar da ke tsakanin Nijar da Faransa, ta fannin ma'adinai da tsaro domin saka haske kan dumbin arzikin da ta jima tana hakowa a cikin tsarin yarjejeniyar cudeni-in-cudeka.

Masanin tattalin arzikin Nijar Issoufou Kado, cewa ya ke "Faransa na kulla irin wadannan yarjejeniyoyi da ba sa amfanar Nijar kamar yadda ake bukata, kuma tana fakewa da wasu 'yan kasar marasa kishin kasa ta kwashi ganima, ba tare da Nijar din ta ci moriyar dumbin arzikin da Allah ya hore mata ba."

Karin Bayani: Kadawar guguwar sauyi a yammacin Afirka

Nijar ce kasa ta uku a yankin Sahel da ta bukaci Faransa ta fice mata daga kasa, bayan Burkina Faso da Mali da ke makwabtaka da ita, wanda hakan ya kara fitowa karara da irin kyamar da ake nuna wa Faransa ta fannin rashin saka adalci da gurbatacciyar mu'amala a tsakaninta da sauran kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.Duk da dumbin arzikin da Allah ya albarka ci Nijar har yanzu kasar ce ke zama ta karshe daga jerin kasashen duniya mafiya raunin tattalin arziki, lamarin da ke ci wa dumbin 'yan kasar tuwo a kawarya.