1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta kori jakadan Faransa a kasarta

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2023

Cikin wata sanarwa da ta fitar ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Nijar, ta bukac jakadan Faransa Sylvain Itté ya ya hada komatsantsa ya bar kasar cikin sa'o'i 48.

https://p.dw.com/p/4Vb5q
Nijar | Yamai | Zanga-Zanga | Kyama | Faransa | Juyin Mulki
Faransa na fuskantar zanga-zangar nuna kyama, tun bayan juyin mulkin na NijarHoto: AFP/Getty Images

Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Nijar din dai ta ce, ta dauki wannan mataki ne saboda jakadan na Faransa Sylvain Itté ya ki amsa gayyatar taro da ministan harkokin kasashen ketare na Nijar din ya aike masa. Sanarwar ta kuma ce baya ga wannan dalilin, akwai kuma wasu mataka da gwamnatin Faransan ke dauka da ba su yi daidai da muradun Nijar din ba. Sai dai kuma sanarwar, ba ta yi wani karin haske kan matakan ba. Tun dai bayan da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne, sojojin na Nijar suka fara takun saka da uwar gijiyarsu Faransa da ta yi musu mulkin mallaka. Kawo yanzu dai ma'aikatar harkokin kasashen ketaren ta Faransa da ke zaman guda cikin kasashen da suka bukaci a mayar da gwamnatin dimukuradiyya a Nijar din, ba ta ce komai ba kan bukatar gwamnatin juyin mulkin sojan.