1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar kashe Bazoum daga sojoji

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 10, 2023

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, sun sha alwashin kashe hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum in har makwabtan kasashe suka yi yunkurin daukar matakin soja a kansu domin mayar da shi kan mulki.

https://p.dw.com/p/4V199
Nijar | Yamai | Mohamed Bazoum | Juyin Mulki
Hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da ke rike hannun sojojiHoto: Boureima Hama/AFP/AP/dpa/picture allaince

Kamfanin dillancin labaran Amurka na Associated Press ya ruwaito cewa, wakilin sojajin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar ta Nijar, ya shaidawa karamar sakatariyar harkokin kasashen ketare ta Amurka Victoria Nuland hakan yayin wata ziyara da ta kai Nijar din. Duk wani mataki na sasanta wa da sojojin dai ya ci tura, inda suka hana kowa ya samu damar ganin jagoran juyin mulkin. Ita kanta Nuland ba a amince ta ga jagoran juyin mulkin ko hambararren shugaban ba lokacin ziyarar tata, yayin da aka ki amince wa wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar Tarayyar Afirka AU da ma na kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO zuwa kasar baki daya. Ko da yake an hango jagoran juyin mulkin Abdourahmane Tchiani yana ganawa da Sarkin Kano na 14, kana shugaban darikar Tijjaniya Khalifa Muhammad Sanusi na II da ya jagoranci wata tawagar Najeriya zuwa Yamai.