1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Daliban Kuriga sun sake tozali da iyalansu

Fauziyya Dauda Abdoulaye Mamane/Abdul-raheem Hassan
March 28, 2024

Hukumomi a jihar Kaduna sun yi alkawarin sake gina makarantun Kuriga da samar musu da wasu muhimman wuraren more rayuwa da ba wa daliban da aka yi garkuwa da su tallafin karatu kyauta

https://p.dw.com/p/4eEKv
Mahaifan daliban Kuriga da aka sace na shirin tozali da yaransu
Mahaifan daliban Kuriga da aka sace na shirin tozali da yaransu Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Hukumomi a jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun sake mika dalibai 137 da aka yi garkuwa da su a hannun mahifansu bayan kammala binciken lafiyarsu, gwamnatin jihar ta yi alkawarin sake gina makarantun firamari da sakandiren yankin, da daukar nauyin karatun daliban, kana gwamnan Kaduna Uba Sani ya yi alkawarin ba wa iyalan malamin makarantar nan Abubakar Isah, da ya rasu hannun 'yan bindiga tallafin miliyan naira miliyan 10. 

Fiye da yara 'yan makarantar Kuriga 130 da aka ceto daga hannun 'yan bindiga aka mika su ga iyayensu kuma ake sa ran su koma gida a wannan Alhamis din.

Karin bayani:  Sojin Najeriya sun kore alkaluman farko na sakin daliban Kuriga

An hada yaran ne da iyayensu a wajen wani taro da Gwamna Uba Sani a wannan Laraba. Mai magana da yawun gwamnan jihar, Muhammad Shehu ya ce an mika dalibai 137 din ne bayan da aka kammala duba lafiyarsu, sai dai kuma malaminsu da aka sace tare da daliban ya rasu.

Wasu daga cikin daliban da aka sace daga Kuriga
Wasu daga cikin daliban da aka sace daga KurigaHoto: Chinedu Asadu/AP Photo/picture alliance

A ranar bakwai ga watan Maris din wannan shekara 'yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 137 a makarantarsu da ke kauyen Kuriga, inda a shekarun baya-bayan nan barayin daji sun yi garkuwa da daruruwan yara da dalibai a sakamakon tabarbarewar tsaro a yankunan Arewa maso Yamma da kuma yankin tsakiyar Najeriya.

Karin bayani:  An saki dukkan daliban Kuriga da aka sace a Najeriya

Dakarun tsaro na ci gaba da kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, sai dai kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci jami'an tsaro da su tabbatar da cewa ba a biya ko sisin Kobo a matsayin kudin fansa ba.