1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Satar mutane na kara samun gindin zama a Najeriya

March 18, 2024

Kimanin mutane 100 aka sace a jihar kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya, sama da mako guda da sace 'yan makaranta wajen 300 a dai jihar ta kaduna, kamar yadda hukumomi suka tabbatar wa da kamfanin AFP.

https://p.dw.com/p/4dsUQ
Sojojin Najeriya a yayin aikin kubutar da daliban Kuriga a Kaduna
Sojojin Najeriya a yayin aikin kubutar da daliban Kuriga a KadunaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan dauke da muggan makamai sun yi  wa yankin na Kajuru kawanya tare da sace mutane da dama, lamarin dai na zuwa a daidai lokacin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen kasar kan yadda ake garkuwa da mutane ba kakkautawa a lokacin gwamnatinsa.

Karin bayani: Sojin Najeriya sun lashi takobin kubutar da daliban Kuriga 

Shugaban karamar hukumar Kajuru a jihar ta kaduna Ibrahim Gajere, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da mutane kimanin 87.

Karin bayani: Tinubu ya yi watsi da biyan kudin fansa ga 'yan fashi

Yankin na Kajuru na da nisan kilomita 150 wato mile 93 kenan daga garin Kuriga da aka sace dalibai kimanin 250 a farkon wannan watan na Maris.