1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojoji sun kore alkaluman farko na sakin daliban Kuriga

March 24, 2024

Kimanin dalibai 137 daga cikin kusan 300 da 'yan bindiga suka sace a Kuriga da ke jihar Kaduna aka sake su, acewar ma'aikatar tsaron Najeriya.

https://p.dw.com/p/4e4VQ
Sojojin Najeriya a yayin sintirin neman daliban Kuriga
Sojojin Najeriya a yayin sintirin neman daliban KurigaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Hakan ya kore sanarwar da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar tun da fari na cewa an saki dukkan daliban na makarantar Kuriga da ke hannun 'yan ta'adda. A ranar 7 ga watan Maris 2024, 'yan bindiga dauke da muggan makamai suka yiwa garin na Kuriga kawanya tare da sace daliban makarantun firamare da sakandare da ke kauyen.

Karin bayani: Tinibu ya yi Allah wadai da sace dalibai

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Maj. Gen. Edward Buba, ya ce sun yi nasarar kubutar da daliban su 137 daga wani yanki na jihar Zamfara da ke da nisan kilomita 124 daga garin na Kuriga.

Karin bayani:Satar mutane na kara samun gindin zama a Najeriya 

Ya kara da cewa zasu ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kubutar da sauran daliban tare da cafke dukkan 'yan ta'addan domin su fuskanci shari'a.

Karin bayani: Kaduna: Ko daliban da aka sace za su tsira?

Dalibai sama da 1,400 aka sace a sassa daban-daban na kasar tun bayan sace daliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.