1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Ukraine na kai ruwa rana da Rasha

Suleiman Babayo ZMA
February 26, 2022

Sojoji Rasha da ke mamaya a kasar Ukarine suna ci gaba da kaddamar da hare-hare manyan makamai tare da fafatawa da sojojin Ukraine da ke ci gaba da jan-daga.

https://p.dw.com/p/47dVX
Ukraine Konflikt
Hoto: Gleb Garanich/REUTERS

Dakarun Rasha suna ci gaba da kaddamar da hare-hare a Kiev babban birnin kasar Ukraine, inda ake ci gaba da jin karar abubuwa masu fashewa, kana rundunar sojin kasar ta Ukraine ta ce sojojin Rasha sun kaddamar da sabbin hare-hare da makamai masu linzami daga cikin teku. Hare-haren sun ritsa da daruruwan mutane, yayin da mazauna babban birnin suka buya a gine-ginen gidaje da makarantu gami da karkashin kadoji.

Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar ta Ukraine wanda makomarsa ke cikin mawuyacin hali ya ce biranen kasar suna karkashin matsanancin hare-hare, bayan tun farko ya bukaci tsagaita wuta. Sannan ya ce babu gudu babu ja-da baya.

Yayin da ake ci gaba musanyen wutar dakarun Ukraine sun bayyana kakkabo jirgin saman yakin Rasha na biyu wanda yake dauke da sojojin Rasha a gari mai nisan kilo-mita 25 daga birnin Kiev fadar gwamnatin kasar, abin da wani babban jami'in leken asiri na Amirka ya tabbatar. Kawo yanzu ba a tantan ce yawan dakarun Rasha da ke cikin jiragen saman da aka kakkabo ba. Sai dai ana rade-radin lamarin ya ritsa da daruruwan dakarun na Rasha.