1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Macron zai gana da Putin a Moscow

Binta Aliyu Zurmi
February 7, 2022

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa Rasha domin ganawa da takwaransa Vladmr Putin a fadarsa ta Kremlin. Ganawar za ta mayr da hankali ne kan rikicin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/46dln
Frankreich Bormes-les-Mimosas | Putin trifft Macron in Südfrankreich
Hoto: Alexei Druhzhinin/AFP/Getty Images

Shugaba Macron shi ne shugaba na farko daga kasashen yamma da zai yi ganawar keke da keke da Putin tun bayan da wannan rikici ya barke a watan Disamba shekarar da ta gabata.

Macron na fatan wannan tattaunawa da zai yi da Putin ta kawo karshen wannan rikicin da kasashen yamma ke ciki da Rasha wanda ba a ga irin shi ba tun bayan yakin chachar baka.

A gobe Talata kuma Mr. Macron zai isa birnin Kyiv na Ukraine inda a can ma zai tattauna Shugaba Volodmyr Zelensky, a kokarin da ake yi na ganin an rikcin cikin ruwan sanyi.

Wannan yunkuri na Macron dai na zuwa ne daidai lokacin da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ke ziyara a Amirka son ganawa da ShugabaJoe Biden a fadar mulki ta White House kan rikicin na Ukraine.