1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin warware rikicin Rasha da Ukraine

Ahmed Salisu
December 9, 2019

An fara gudanar da wani shiri na musamman don warware takun sakar da ake fama da ita tsakanin Rasha da Ukraine kan rikicin gabashin Ukraine.

https://p.dw.com/p/3UVvN
Frankreich Normandie | Gipfeltreffen: Vladimir Putin, Angela Merkel, Emmanuel Macron und Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Getty Images/AFP/I. Langsdon

Shugaban Vladmir Putin na Rasha da shugaban Ukraine Volodomyr Zelensky sun shirya yin wata tataunawa da tawarawansu na Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwmanatin Jamus Angela Merkel da nufin lalubo hanyoyin da za a bi wajen warware takun sakar da ke akwai tsakanin Rasha da Ukraine.

Shugaba Zelensky na Ukraine da ya hau gadon mulki a farkon wannan shekarar ne dai ya mika goron gayyata ga Shugaba Putin kan a yi wannan zama don warware wannan zaman doya da na manja da ake yi.

Wannan zama dai na zuwa ne daidai lokacin da Kungiyar EU ke shirin sabunta takunkumin da ta kakabawa Rasha saboda hannun da ta ce tana da shi a rikicin na gabashin Ukraine.