1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da kai farmaki Gaza

December 14, 2023

Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da ragargazar yankin Gaza duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na tsagaita bude wuta da hakan ke ci gaba da jawo hasarar rayukan dubban al'umma a yankin.

https://p.dw.com/p/4a8Qu
Hoto: Ohad Zwigenberg/AP/picture alliance

Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da ragargazar yankin Gaza duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na tsagaita bude wuta da hakan ke ci gaba da jawo hasarar rayukan dubban al'umma a yankin ciki kuwa har da wasu daga cikin kawayen Isra'ilan a Amurka.

Isra'ila dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya harma da Majalisar Dinkin Duniya na dakatar da kai hare-haren soji kan galibi fararen hula dake Gaza, inda a baya bayan nan mambobi 153 daga cikin 193 suka kada kuri'ar amincewa da tsagaita bude wuta a  zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma nuna fargabarta kan bullar cututtuka a yankin na Gaza irinsu sankarau da amai da gudawa da kuma sauran cututtuka da suke shafar numfashi sakamakon gurbacewar muhalli.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun na Isra'ila sun kaddamar da sabbin hare-hare a birnin Gaza da Khan Yunous da kuma Rafah dake kudanci.