1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan Jamus a Chadi ya fice daga kasar

Abdoulaye Mamane Amadou
April 9, 2023

Bayan ba shi wa'adin sa'o'i 24 da ya fice daga kasar, jakadan Jamus a kasar Chadi ya fice daga babban birnin kasar N'Djamena a yammacin wannan Asabar

https://p.dw.com/p/4Pr31
Tschad | Mahamat Idriss Déby, Präsident des Übergangs-Militärrates (CMT)
Hoto: Brahim Adji/Tchad Presidential Palace/AFP

Jakadan jamus a kasar Chadi ya fice daga babban birnin kasar a yammacin jiya, jim kadan bayan da fadar mulki ta birnin N'Djamena, ta bukaci Jan Christian Gordon Kricke ya fice mata daga kasa a cikin sa'o'i 24.

Ma'aikatar harkoklin wajen Chadin ce ta tabbatar da haka a yau a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinta Aziz Mahamat Saleh. Chadi ta zargi jakadan Jamus din da katsalandan a cikin harkokinta na cikin gida, abinda ta kira ka iya gurbata zaman takewa a tsakanin 'yan kasar.