1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Bin Salman ya bukaci tsagaita wuta a Gaza

March 11, 2024

Mutanen Gaza sun fara Azumin Ramadan cikin yaki da bala'in yunwa sakamakon kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a dan karamin yankin na Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4dNFb
Yarima Salman ya kira da a tsagaita wuta a Gaza
Yarima Salman ya kira da a tsagaita wuta a GazaHoto: Sergei Savostyanov/Sputnik/REUTERS

Yarima Muhammad Bin Salman ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen ta'asar da ake tafkawa a yankin zirin Gaza, a daidai lokacin da al'umma musulmi a Saudiyya da yankunan Falasdinawa da kuma wasu kasashen musulmi da dama suka wayi garin wannan Litinin da Azumin watan Ramadan.

Yariman na Saudiyya ya yi wannan kira ne a jawabinsa na sanar da ganin watan Ramadan da yammacin Lahadi, inda ya bukaci kasashen masu karfin fada a ji da su kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza tare da gaggauta samar da hanyoyin shigar da kayan agaji ga al'ummar yankin da ya fara fama da yunwa. 

Karin bayani: Amurka ta aike da jirgin dakon kaya na ruwa dauke da kayan agaji Gaza

Har kawo wannan lokaci duk wani kokari na samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin na Gaza ya ci tura, hasali ma ko da a ranar Lahadi dakarun Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a dan karamin yankin na Falasdinu da ya fada yaki sama da watanni biyar da suka wuce.