1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bambanci tsakanin ECOWAS da UEMOA

November 4, 2011

ECOWAS ta kunshi kasashen yammacin Afirka 15 ,UEMOA ta kunshi kasashe takwas na yammacin Afirka masu amfani da kudin CFA

https://p.dw.com/p/135S9
Mohammad Ibn Chambas tsofan shugaban ECOWAS a tattanawar bunkasa kungiyarHoto: picture-alliance / dpa/ dpaweb


ƙungiyoyin ECOWAS da UEMOA sun bambanta, ko wace da matsayinta da burin da ta sa gaba duk da cewa yankin guda suke wato yankin yammacin Afrika.

Ita dai ECOWAS kokuma CEDEAO ƙungiya ce wadda ta haɗa dukkan ƙasashe 15 na yankin yammacin Afrika da su 16 ne ma har da Mauritaniya amma daga bayan sai Mauritaniya ta hita su ka koma 15.

An girka wannan ƙungiya tun shekara 1975 wato yanzu shekaru 36 kenan.Cibiyar ECOWAS ta nan birnin Abuja na Najeriya.

Babban burin da wannan ƙungiya ta sa gaba shine haɓɓaka tattalin arzki da kyautata rayuwar jam´ a dake rayea cikin wannan ƙasashe 15 ta hanyar cuɗe ni in cuɗe ka.Ana iya kwatanta ECOWAS kokuma CEDEAO da ƙungiya kamar ƙungiyar Tarayya Turai wato EU.

Idan aka ɗauki misalin ƙungiyoyin dake yankuna dabamdaban na Afirka, dukansu ECOWAS ta fi su tsari kuma ta hi su gudanar ada aiyuka da cude ni in cude ka, tsakanin ƙasasahe membobi.

Baban babamci tsakanin ECOWAS da UEMOA shine, yanzu na ce ECOWAS ta ƙunshi ƙasashe 15, ita kuwa UEMOA ƙasashe takwas ne kawai membobinta wato Jamhuriya Nijar, Mali, Benin,Senegal , Burkina Faso,Cote´d´Ivoire,Togo da Guinea Bissau, amma ita Guinea Bissao daga baya ne ma ta shiga.

UEMOA ƙungiya ce wadda ta ƙunshi ƙasashen yankin yammancin Afrika zalla masu amfani da kuɗin CFA.

An girka ta a shekara 1994, a birnin Dakar na ƙasar Senegal.Da ƙungiyar UMOA aka kiranta, abinda ya haɗa ƙasashe membobinta da farko shine kawai takardar kuɗin CFA to amma a shekara 1994 aka sake raɗa mata suna zuwa UEMO wato a ƙara harafin E, wanda ke ma´anar tattalin arziki, banda batun kuɗi ƙungiyar ta kuma tanadi haɗa ka, ta fannin tattalin arziki tsakanin ƙasashe takwas membobinta.daga cikin wannan ƙasashe takwas bakwai dukansu kasashe ne anda Faransa ta yi wa mulkin mallaka, domin akwai yarjeniyar kudi tsakanin Faransa da ƙasashen Afirka da tay i wa mulkin mallaka.Ƙasar Guinea Bisau ce kaɗai renon Portugal bare daga cikin ƙungiyar, amma duk da haka ta shiga UEMOA domin ta fahinci cewar tatalin arzikinta sai fi bunƙasa idan ta haɗa kai da wannan ƙasashe.Ita cibiyar UEMOA ta na birnin Ouagadougou na Burkina Faso.

Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman