1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaZambiya

Ana zakewa da shan maganin kashe kwayoyin cuta

Muntaqa Ahiwa Abdoulaye Mamane(LMJ)
March 20, 2024

Masu ruwa da tsaki kan harkokin lafiya a Zambiya, na nuna damuwa kan karuwar yawan shan magungunan kashe kwayoyin cuta da ake samu a kasar, saboda yadda mutane ke yawan amfani da su.

https://p.dw.com/p/4ZMDr
Medikamentemangel in Deutschland
Hoto: imago images

Ministar lafiya ta kasar Zambiya Sylvia Masebo ta bayyana tsananin matsalar bijire wa magani da ake samu yanzu a tsakanin mutane a Zambiya, matsalar kuwa da ke da nasaba da matsa wa shan magungunan kashe kwayoyin cutar bacteria da mutane ke yi.

Miliyoyin mutane a cewar hukumomi da jami'an lafiya ke wannan garaje, inda suke dirkar magungunan kan matsalolin da ba su bukatar magungunan antibiotics a likitance.Ana iya ganin mutane kan sayo magungunan lokacin da suke fama da hatta mura ko ciwon kai, inda wasun su ke matsa wa jami'an lafiya da lallai a ba su domin su sha.

Wannan matsalar ta sanya kwararru masu yaki da dabi'ar shan magunguna ba bisa ka'ida ba irin su Kyembe Ignitius Salachi,ke nuna takaicin sa, yana mai cewa " Akwai wani tunani da ake da shi, cewar magungunan kashe kwayoyin cutar bacteria na aiki nan take, musamman ga mutanen da aka bai wa su saboda magance wata matsalar kuma ya yi musu aiki. Tunanin shi ne yadda maganin ya warkar da cutar da likita ya bayar a kai, haka ne zai yi wa kowace larura."Kyembe Ignitius Salachi, na dora alhakin yawaitar shan magungunan ne a kan rashin tsanani daga gwamnati da ma karancin fadakarwa ga jama'a.

Haka ma dalibin da ke karatun aikin likita a jami'ar Zambiya da ke a Lusaka babban birnin kasar, ra'ayinsa ne shi ma cewa akwai sakacin daga mahukunta abin da ke kara matsalar bijire wa magunguna da jikin mutane ke yi a Zambiya, musamman matasa.

 "Akwai bukatar a kara dagewa ga fadakar da jama'a kan matsalar bijire wa magungunan kashe kwayoyin cutuka da tabbatar da aiwatar da dokoki da sauran tsare-tsaren da suka shafi amfani da magunguna irin wadannan.”

Dakin sayar da magunguna
Dakin sayar da magunguna Hoto: Nyani Quarmyne

Gagarumar bukatar masu fafutakar kawo karshen wannan matasala dai a Zambiya, ita gwamnati ta kafa dokoki masu tsauri a kan shagunan sayar da magunguna, ta yadda za a daina sayar da su barkatai ga jama'a, in banda wadanda suka kawo takardu da likitoci suka bayar. Kyembe Ignitius Salachi, na cikin wadanda suke wannan da'awa, yana mai cewa

 "Karfafa dokoki kan sayar da magunguna, musamman ma wadanda kantuna kan bayar ba tare da takarda daga likita ba. Lallai ne a haramta bayar da magungunan antibiotic ba tare da shaida daga asibiti ba, kuma almuhimmi shi ne duk wani mai sayar da magani da da ak samu ya karya dokar, to ya fuskanci fushin hukuma.” 

Masu wannan gwagwarmayar a Zambiya dai sun kafe tare da matsawa kan kiraye-kirayen mahukunta kasar da su yi hanzarin taka wa matsalar shan magungunan na antibiotics ba bisa ka'idar ba burki, ganin fadin da take yi da ma hadarinta ga lafiyar al'uma.