1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai sabbin hare hare wajen Kyiv

July 29, 2022

A karon farko cikin 'yan makonnin da suka gabata Rasha ta kai sabbin hare hare da makamai masu linzami da suka fada wajen birnin Kyiv. Sai dai Ukraine ta ce ta kaddamar da harin ramuwar gayya.

https://p.dw.com/p/4Ep0c
Ukraine Raketenangriff auf eine Militäreinheit im Bezirk Wyschhorod am Stadtrand von Kiew
Hoto: David Goldman/ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Sojojin Rasha sun kai harin makamai masu linzami wani yanki kusa da Kyiv babban birnin kasar Ukraine a ranar alhamis a karon farko cikin 'yan makonni da wuce.

Akalla mutane 15 suka jikkata sakamakon harin biyar daga cikin su fararen hula a cewar gwamnan Kyiv Oleksiy Kuleba.

Rahotanni sun ce harin ya lalata wani wuri a arewacin Chernihiv a wani abin da Ukraine din ta baiyana da cewa huce haushi ne sakamakon jajircewar da sojojinta suka yi na hana Rasha samun galaba.

A waje guda kuma hukumomin na Ukraine sun ce sun kaddamar da farmaki domin kwato yankin Kherson a kudancin kasar da Rasha ta mamaye.