1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun kasa da kasa

January 12, 2024

Kasar Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun kasa da kasa ta ICJ da ke Haque, domin kare kan ta tare da martani kan wadanda ke zarginta da aikata laifukan yaki da kuma kisan kare dangi a yakin da ta ke yi da Hamas a Gaza.

https://p.dw.com/p/4b9Zc
Hoto: THILO SCHMUELGEN/REUTERS

A kwanaki na biyu na shari'ar da aka soma jiya Alhamis 11 ga watan Janairu, 2024, kotun ba za ta yanke hukunci ba kan korafe-korafen da aka shigar a gaban ta, na cewa shin Isra'ila na aikata kisan kare-dangi a Gaza, amma za ta duba batun 'yanci na al'ummar Gazan ko ya na cikin hadari.

A baya-bayannan ne kasar Afrika ta Kudu ta shigar ta korafin gaggawa na dakatar da Isra'ila daga kisan kiyashin da ta ke yi a Gaza, kasancewar hakan ya ci karo da yarjejeniyar MDD da kasashe suka rattaba hannu a 1948, biyo bayan kisan kiyashin da aka yiwa yahudawa lokacin yakin duniya na biyu da aka fi sani da Holocaust.

A martanin da ya mayar kan karar da Arfika ta Kudu, ta shigar gaban kotun ICJ,  Firaimistan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce ya na son Afrika ta Kudu ta san cewa, ba su suka assasa kisan kare dangin ba, Hamas ce.

Ministan shari'a na kasar Afrika ta Kudu Ronald Lamola, ya shaida wa kotun cewa kasar Isra'ila, ta ketare iyaka kuma hakan ya ci karo da yarjejeniyar da aka cimma.