1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Gamane ta kashe mutum 11 a Madagascar

March 28, 2024

A kalla mutane 11 ne aka tabbatar da mutuwarsu a tsibirin Madagascar sakamakon guguwar Gamane da ta tunkari kasar.

https://p.dw.com/p/4eDy2
Guguwar Gamane ta kashe mutum 11 a Madagascar
Hoto: Alkis Konstantinidis/REUTERS

Rahotannin sun yi nuni da cewa, kimanin mutane 7,000 ne iftila'in ya shafa a kudu maso gabashin tsibirin Madagascar. Hukumomi a kasar na cewa guguwar na gudun kilomita 150 a kowace sa'a daya yayin da a wasu yankunan take gudun kilomita 210 a kowace sa'a.

Hukumar kare aukuwar bala'o'i ta kasar ta ce guguwar da ta taho tare da ruwan sama mai karfin gaske, ta haifar da lalacewar daruruwan gidaje da hanyoyi da kuma gadoji a arewacin kasar. Kawo yanzu dai ba a kammala tantance hasarar da iftila'in ya haifar ba sakamakon wasu kauyukan sun rabe da kasar, lamarin ya sanya jami'an agaji ba su iya isa irin wuraren. Tsibirin Madagascar da ke nahiyar Afirka mai yawan al'umma kimanin miliyan 30 na yawan fuskantar matsaloli na yanayi.

Ko a shekarar bara, mahaukaciyar guguwar Freddy ta afkawa kasar da kuma makwaftanta Mozambique da kuma Malawi, wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane fiye da 500.