1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: An haramtawa 'yan adawa tsayawa takara

March 24, 2024

Hukumomi a kasar Chadi sun haramta wa wasu 'yan adawa tsayawa takara a zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/4e4g6
Shugaban rikon kwarya na Chadi, Mahamat Deby Itno
Shugaban rikon kwarya na Chadi, Mahamat Deby ItnoHoto: Mikhail Metzel/dpa/AP/picture alliance

Hukumomi a kasar Chadi sun haramtawa 'yan takara 10 daga neman kujerar shugaban kasa a zaben da za a gudanar a watan Mayaun wannan shekarar. Daga ciki wadanda aka dakatar har da mutum biyu daga cikin masu adawa da majalisar mulkin sojin kasar, yayin da sauran 'yan takara 10 da kotun tsarin mulkin kasar ta amince da takararsu har da shugaban gwamnatin mulkin soji Mahamat Idriss Deby Itno da kuma Firanminista Succes Masra.

Karin bayani:Mahamat Deby zai yi takarar shugabancin Chadi a 2024 

Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kasar Chadi da shugaban kasa da kuma Firanminista za su tsaya takarar neman dare wa kan madafun ikon kasar a lokaci guda. Sai dai 'yan adawa na cewa, Masra ya tsaya takara ne kawai domin ya halasta da zaben. Ana dai ganin Mahamat Deby ya samu nasara a zaben sakamakon manyan abokan hammayarsa sun mutu ko kuma su na gudun hijira. Ana sa ran a gudanar da zagayen farko na zaben a ranar 6 ga watan Mayu da kuma zagaye na biyu a ranar 22 ga watan Yunin wannan shekarar.