1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso na shirin daina amfani da kudin CFA

Binta Aliyu Zurmi
February 1, 2024

Kasar Burkina Faso na duba yiwuwar janyewa daga jerin kasashen Afirka ta Yamma rainon Faransa masu amfani da kudi na bai daya na CFA.

https://p.dw.com/p/4buVa
Banknoten CFA Francs
Hoto: SEYLLOU/AFP

Kasar Mali ta bayyana cewar ba ta da niyyar daukar wannan mataki na daina amfani da kudin bai-daya sabanin Burkina Faso da ta nuna aniyyar raba gari da takardar kudin.

Ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Dioup ne ya bayyana hakan, bayan kasar Burkina Faso ta sanar da wannan mataki tun bayan da suka sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWASmai mambobi 15.

Wannan kwan-gaba kwan-baya a kan kudi naCFA da aka jima ana yin shi ya jefa kasashe mambobin kungiyarUEMOA 8 da ke amfani da kudin cikin hali na rashin sanin tabbas a game da makomarsu.

Kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da dukkaninsu ke amfanin da kudin na CEFA na a karkashin mulkin sojoji ne, wanda kuma a baya-bayan nan suka sanar da ficewarsu daga kuungiyar raya tattalin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, wanda har yanzu suke kai ruwa rana da shugabnnin kungiyar na kin amincewa da wannan mataki na su.