1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantakar Faransa da Mali

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 10, 2023

Kasanshen Faransa da Mali sun dakatar da bayar da takardar izinin shiga kasashensu wato visa ga juna, abin da ke nuna yadda dangantaka ke kara tsami a tsakanin kasashen da suka kasance kawayen juna a baya.

https://p.dw.com/p/4V0Wy
Mali | Faransa | Dangantaka | Tsami
Tuni dai sojojin Faranasa suka hada komatsansu tare da ficewa daga MaliHoto: Etat-major des armées / France

Ofishin jakadancin Faransa a Bamako ya bayyana cewa, ya dakatar da bayar da sababbin takardun izinin shiga kasa wato visa ga 'yan Mali da ke son zuwa Faransan a farkon wannan makon, bayan Paris ta sanya Malin a matsayin kasa mai hadari tare da bai wa 'yan kasarta shawarar ka da su ziyarta. Rahotanni sun nunar da cewa, Faransan ta kuma dakatar da bayar da izinin shiga kasarta ta a daya tsohuwar aminiyar tata a yankin Sahel wato Burkina Faso. Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da sojoji suka kifar da gwamnati a makwabciyar Malin wato Jamhuriyar Nijar da ke zaman babbar kawa ga Faransan.